Isa ga babban shafi

An yi cacar baka tsakanin jakadun Iran da Isra'ila a zauren MDD

Kasashen Iran da Isra’ila sun zargi juna da zama barazana ga zaman lafiyar yankin gabas ta tsakiya, inda ko wacce ta yi kira ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya da ya ƙaƙaba wa ɗayansu takunkumi.

Zauren Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya yayin cacar bakan da ta kaure tsakanin jakadun kasashen Iran da Isra'ila.
Zauren Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya yayin cacar bakan da ta kaure tsakanin jakadun kasashen Iran da Isra'ila. AP - Yuki Iwamura
Talla

Wannan na zuwa ne bayan da Iran ta kaddamar da harin ramuwar gayya kan Isra'ila a ranar Asabar, inda ta harba jirage marasa matuka da makamai masu linzami fiye da 300.

Tun a karshen makon da ya gabata sojojin Isra’ila suka bayyana dakile kusan kashi 99 cikin 100 na harin da Iran ɗin ta kai musu cikin dare.

Sai dai rundunar sojin Iran ɗin ta ce sun cimma nasarar da suke nema.

Wannan lamari dai ya haifar da fargaba a yankin Gabas ta Tsakiya game da yiwuwar barkewar sabon yaƙi, muddin Isra’ila ta sake kai wa Iran farmaki domin daukar fansa.

A ranar Lahadi Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya kira taron gaggawa domin lalubo bakin zaren warware sabon rikicin da ke neman kunno kai tsakanin kasashen da suka daɗe suna gaba da juna.

Yayin taron Kwamitin Tsaron ne jakadan Iran Amir Saeid Iravani, ya nanata cewa kasarsa ta yi amfani da damarta ne wajen kare kanta.

Shi ma takwaransa na Isra’ila Gilad Erdan, ya bukaci kwamitin tsaron da ya kakaba wa Iran takunkumai, bayan harin ramuwar gayyar da ta kai musu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.