Isa ga babban shafi
Saudiya - coronavirus

Babu wanda ya harbu da korona cikin Mahajjata - Saudiya

A yayin da mahajjata ke shirin Ibadan hawar Arafat ranar Litinin, hukumomin Saudiya sun tabbatar da cewa babu wani mani daga cikinsu da ya harbu da annobar korona, dai-dai lokacin da kasar ta samu sabbin mutane 12 da cutar ta kashe ranar Lahadi wanda yah aura adaddin wandanda cutar ta kasahe zuwa dubu 8,075 a fadin kasar.

Dakin Kaba'a dake Makkatul Mukarrama na kasar Saudiya, inda mahajjata 60 kachal ke sauke farali saboda korona, 19-07-21
Dakin Kaba'a dake Makkatul Mukarrama na kasar Saudiya, inda mahajjata 60 kachal ke sauke farali saboda korona, 19-07-21 - AFP
Talla

Ma’aikatar Kiwon Lafiyar kasar Saudiya tace an samu sabbin mutane 1,055 da suka harbu da cutar cikin sa’o’i 24 da suka gabata, wanda ya haura jummular adadin mutanen suka harbu da cutar zuwa dubu 509,576 a kasar.

Hukumomi suka ce akasarin sabbin kamuwar an same su ne a birnin Riyadh, inda aka sama da muatane 323 suka harbu, sai kuma birnin Makkah da yanzu haka mahajja kimanin dubu 60 ke aikin sauke farali aka samu mutane 187 da suka harbu, to sai dai, ma’aikatar lafiyar kasar ta tabbatar da cewa babu ko da mutun guda da ya harbu da cutar cikin mahajjata.

Sauran biranen da sabbin harbuwar ya shafa sun hada da Lardin gabas inda mutane 170 suka harbu, sai kuma Asir da mutane 114 sannan kuma Qassim da mutane 66 da suka harbu cikin sa’o’i 24 wato ranar Lahadi kaidai.

Humomin sun sabunta kirar al’umma da su ci gaba da rajistan karbar allurar rigakafin koronar da yayi sanadiyar kashe sama da mutane dubu 8,075 a kasar.

A bangare daya jami’an tsaron saudiyar sun sanar da tsare mutane 64 da suka karya dokar killacewa, bayan gwaji ya tabbatar suna dauke da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.