Isa ga babban shafi
Taron kasashen Gabas ta Tsakiya

Macron na cikin shugabannin da suka halarci taron kasashen Gabas ta Tsakiya

Shugaban Faransa Emmanuel Macron na daga cikin shugabannin da ke shirin halartar wani taron yankin Gabas ta Tsakiya yau Asabar a Iraki, inda ake ganin batun kwace ikon Afganistan da Taliban tayi da kuma mummunan harin ta’addanci a Kabul zai mamaye taron.

Franministan Iraki Mustafa al-Kadhemi tare da bakin da suka halarci taro cikin harda shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi.
Franministan Iraki Mustafa al-Kadhemi tare da bakin da suka halarci taro cikin harda shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi. - IRAQI PRIME MINISTER'S PRESS OFFICE/AFP/File
Talla

Sabon Shugaban Jamhuriyar Iran Ebrahim Raisi ya karbin goron gayyatar taron na Bagadaza, amma babu tabbas ko zai halarci taron.

Iraki dake neman zama mai shiga tsakanin kasashen Larabawa da Iran, ta kira taron na wannan Asabar domin neman hada kai da magance rikicin da ke girgiza yankin na Gabas ta Tsakiya.

Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi da sarkin Jordan Abdullah na biyu sun bayyana anniyarsu na halartar taron, haka zalika ana saran zuwan shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, a matsayin shugaban kasa ko babban jami'i dake wajen yankin da zai halarcin taron.

Majiyoyin da ke kusa da Firayim Ministan Iraki Mustafa al-Kadhemi, sun ce an kuma gayyaci shugabannin Saudiyya da Turkiyya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.