Isa ga babban shafi

Kasashen Larabawa na taro karon farko bayan gyara alakar wasunsu da Isra'ila

Kungiyar kasashen larabawa na taro a Algeria, taron da ke zuwa karon farko tun bayan da wasu daga cikinsu suka fara gyara huldarsu da Isra’ila lamarin da ke kokarin haddasa sabanin fahimta.

Taron kasashen Larabawa a Algeria.
Taron kasashen Larabawa a Algeria. via REUTERS - TUNISIAN PRESIDENCY
Talla

Tun bayan taron kasashen larabawan na 2019 wasu daga cikin mambobin kasashen 22 suka kawar da gabar gomman shekaru tare da gyara alakarsu da Isra’ila wadda a baya suka juyawa baya saboda goyon bayansu ga ‘yancin yankin Falasdinu.

Hadaddiyar Daular larabawa ce kasa ta farko bayan Masar da Jordan da suka dawo da huldar da Isra’ila bayan shiga tsakanin da Amurka ta yi wanda ya kai ga kulla yarjejeniyar gyara alakar.

Matakin Daular larabawan ana ganin shi ya bayar da kwarin gwiwa ga kasashen Bahrain da Morocco daukar irin wannan mataki na gyara huldar da Isra’ilan Yahudu, yayinda Sudan ke kan hanya bayan kulla yarjejeniya, haka zalika gyara alakar ana ganin shi ya sake zafafa rikicin Morocco da makwabciyarta Algeria.

Taron wanda aka faro shi a jiya, ake kuma shirin karkarewa a karshen mako, an sha dage lokacin gudanar da shi a baya, saboda annobar corona da sauran matsalolin da duniya ta samu kanta a ciki daga 2019 zuwa yanzu, a wannan karon yana zuwa ne dai dai lokacin da Isra’ila ke zaben sabon Firaminista da ake ganin zai iya dawo da Banjamin Netanyahu kan karagar mulki.

Taron dai zai mayar da hankali kan dawowar alakar kasashen kungiyar kusan 6 da Isra’ila baya ga tabo rikicin da wasunsu ke fuskanta da juna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.