Isra'ila ta kai sabbin hare-hare a kudancin Zirin Gaza
Isra’ila ta kai sabbin hare-hare ta sama a kudancin Zirin Gaza, inda Falasdinawa ke dauka a matsayin tudun mun tsira, bayan tserewa daga arewacin yankin.
Wallafawa ranar:
Ya zuwa yanzu alkaluman jami’an lafiya sun nuna cewar adadin fararen hular da suka mutu a hare-haren na daren jiya ya kai mutane 71, akasarinsu mata da yara.
Bayanai sun ce Isra’ila ta kaddamar da jerin farmakin ne a garuruwan Khan Younis, da Rafah da yayi iyaka da Masar, inda ake fatan daga nan za a bayar da damar fara shigar da kayan agaji zuwa Falasdinawa da suka tagayyara, koda yake har yanzu ba a fayyace lokaci ba.
A wata sanarwa, rundunar sojin Isra'ila ta ce hare-hare sama da 200 ta kai kan kungiyar Hamas cikin daren da ya gabata a fadin zirin Gaza.
A can Isra’ila kuwa, gwamnatin kasar ta ce kimanin mutane dubu 500 aka kwashe daga muhallansu zuwa wasu yankunan, cikin kwanaki goman da suka gabata, bayan farmakin ba-zata mafi muni da mayakan Hamas suka kai mata a ranar 7 ga watan Oktoba.
A wani labarin kuma, kudurin da Rasha ta gabatar wa kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya kan neman kiran tsagaita wuta a yakin Isra’ila da Hamas ya gaza samun kuri’u 9 daga cikin 15 da ake bukata kafin amincewa da shi.
Amurka ce dai ta jagoranci yin fatali da kudurin a bisa hujjar cewa, ya bai wa Hamas kariya ta hanyar kin ambaton farmakin da ta kai wa Isra’ila.
Daftarin na Rasha dai ya yi kira ne da a tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas, a kuma saki fursunonin da aka yi garkuwa da su a Gaza, sai kuma bukatar bai wa fararen hula kariya yayin kwashe su zuwa yankunan tudun mun tsira.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu