Isa ga babban shafi

Kasashen Larabawa sun ce mamayar Isra'ila a yankuna Falasdinawa cin zarafi ne

Kungiyar kasashen Larabawa ta bayyana mamayar da Isra’ila ta yi wa yankunan Falasdinawa a matsayin cin zarafi da kuma karan-tsaye ga dokokin duniya, kuma gazawa wajen dakatar da hakan na iya zama kisan -kare -dangi.

Kungiyar kasashen Larabawa sun bukaci dakatar da mamayar Isra'ila aayankunan Falasdinawa.
Kungiyar kasashen Larabawa sun bukaci dakatar da mamayar Isra'ila aayankunan Falasdinawa. ASSOCIATED PRESS - HASAN JAMALI
Talla

Wakilin kungiyar kasashen Larabawa mai mambobi 22, Abdel Hakim El-Rifai ne ya shaida wa kotun ICC haka a zaman da ta yi a birnin Hague, inda ya ce gazawa da aka yi wajen kawo karshen mamayar ce ta kawo Falasdinawa halin da suke ciki a yau.

Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ta shiga rana ta karshe a sauraron bahasi da take yi bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci haka, kuma kasashe 52 ne ke bada shaidu tare da bayyana ra’ayoyinsu a kan mamayar yankunan Falasdinawa da Isra’ila ke yi.

Akasarin wadanda suka gabatar da jawabi a gaban kotun sun bukaci Isra’ila ta kawo karshen mamayar da ta yi wa Faladinawa, mamayar da ta fara tun bayan yakin kwanaki 6 da aka gwabza a shekarar 1967.

Amma a makon da ya gabata, Amurka ta ce bai kamata a tursasa wa Isra’ila ta janye ba tare da an yi la’akari da batutuwan da suka shafi tsaronta ba.

wadanda suka gabatar da jawabi a kotun a wannan Litinin sun yi kashedin cewa ci gaba da wannan mamaya na tsawon lokaci zai jefa kwanciyar hankalin yankin Gabas ta Tsakiya da ma duniya baki daya cikin hadari.

Akwai yiwuwar kotun ta bayyana hukuncinta a karshen wannan shekarar, amma ba zai kasance tilas dukkannin bangarorin su yi biyayya da shi ba.

Yaki ya barke a Zirin Gaza ne bayan da mayakan Hamas suka kai wani hari kudancin Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya yi sanadin mutuwar sama da mutane dubu daya, akasarin su fararen hula.

Ita ma Isra’ila a martanin da ta ke mayarwa, wanda sai da Amurka ta bayyana a matsayin ‘abin da ya wuce kima’, ta kashe mutane kusan dubu 30 ya zuwa yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.