Mohamed Chia al-Soudani ya bar Bagadaza zuwa Amurka inda zai gana da Joe Biden
Firaministan Iraki Mohamed Chia al-Soudani ya bar Bagadaza a yau Asabar zuwa Amurka inda zai gana da shugaban Amurka Joe Biden, a wani yanayi da ake fuskantar tankiya tsakanin Isra’ila da Iran da kuma yakin Gaza.
Wallafawa ranar:
Fadar shugaban Amurka, ta bayyana cewa Firaministan Iraqi za ya ganawa da Shugaba Biden wanda zai karbi bakuncin shi a ranar litini 15 ga Afrilu 2024.
Firaminista Mohamed Chia al-Soudani ya bar Bagadaza babban birnin kasar zuwa Amurka,ziyarar aiki bisa gayyatar da shugaban Amurka Joe Biden ya yi masa.
Firaministan Iraqi zai halarci taro da Shugaba Biden da nufin tattaunawa a kan magana game da halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya,manufar ita ce "cimma wani jadawalin ƙarshen aikin haɗin gwiwar kasa da kasa da kuma sauye-sauye ga dangantakar da ke tsakanin Iraki da kasashe mambobin kungiyar", a cewar Firaministan Soudani a yau Asabar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu