Isa ga babban shafi

Fararen hula 16 Amurka ta kashe a harin da ta kai Iraqi

Hare-haren da Amurka ta kai a yammacin Iraqi kan kungiyoyin da ke goyon bayan Iran dauke da makamai sun kashe akalla mutane 16 ciki har da fararen hula tare da raunata wasu 23,sanarwa daga kakakin gwamnatin Iraqi Bassem al-Awadi a yau Asabar.

Janar  Patrick Ryder, mai magana da yahun hukumar tsaro ta Amurka
Janar Patrick Ryder, mai magana da yahun hukumar tsaro ta Amurka AP - Kevin Wolf
Talla

 

Bassem al-Awadi a wannan sanarwa ya karasa da cewa Amurka ta yi luguden wuta a yankunan Akashat da Al-Qaim, ciki har da wuraren da jami'an tsaron Iraqi suke.

Amurka ta kai hare-haren a matsayin ramuwar gayya kan kashe jami’an sojan Amurka uku a wani harin da jiragen yaki mara matuki suka kai a sansanin da ke kusa da iyakar Jordan da Syria da Iraqi.

Washington ta dora alhakin harin kan kungiyar Resistance Islamic Resistance a Iraqi,daya daga cikin kungiyoyin da ke adawa da rawar da Amurka da kawanta ke takawa a wannan yanki.Iran dai ta musanta cewa tana da alaka da harin.

Sansanin dakarun Amurka a kan iyaka tsakanin Jordan,Syria da Iraqi
Sansanin dakarun Amurka a kan iyaka tsakanin Jordan,Syria da Iraqi AFP - -

Awadi ya zargi Amurka da "yaudara da kuma kokarin canza gaskiya " ya kuma kira shawarar "da'awar da ba ta da tushe wacce aka shirya don yaudarar ra'ayoyin jama'a na kasa da kasa da kaucewa alhakin shari'a" game da abin da ya ce keta dokokin kasa da kasa ne.

Kakakin ya kara da cewa "Wannan mummunan harin ta sama zai jefa al'amuran tsaro a Iraqi da kuma yankin zuwa cikin wani mawuyacin hali."

Jana'izzar sojojin Amurka da aka kashe a Iraqi
Jana'izzar sojojin Amurka da aka kashe a Iraqi © Joshua Roberts / Reuters

Awadi ya yi Allah wadai da amfani da kasar Iraqi a matsayin filin yaki.,sannan ya sake nanata kiran da gwamnatinsa ta yi na janyewar kawancen kasa da kasa na yaki da Amurka ke jagoranta.

Akwai kusan sojojin Amurka 2,500 da aka jibge a Iraqi da kuma kusan 900 a Sirya a matsayin wani bangare na kawancen da aka kafa a shekara ta 2014 don yakar kungiyar IS,shekarar da kungiyar masu jihadi ta mamaye kusan kashi uku na Iraqi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.