Isa ga babban shafi

Amurka ta fara kai harin ramukon gayya akan Iraqi da Syria dake da alaka da Iran

Sojojin Amurka sun kaddamar da hare-hare ta sama a ranar Juma'a a Iraki da Siriya kan sama da wurare 85 da ke da alaka da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) da mayakan da suke marawa baya, a matsayin ramuwar gayya kan harin da aka kai a kasar Jordan a karshen makon da ya gabata wanda ya kashe sojojin Amurka uku.

Kurman jirgin yakin Amurka
Kurman jirgin yakin Amurka Effrain Lopez/Handout
Talla

 

Hare-haren da suka hada da amfani da bama-bamai masu cin dogon zango sanfurin B-1 da aka tasa daga Amurka, sun kasance na farko a wani martani da gwamnatin Shugaba Joe Biden ta mayar kan harin da mayakan da ke samun goyon bayan Iran suka kai, sannan kuma ana tunanin samun karin hare-haren na sojojin Amurka. ana sa ran a cikin kwanaki masu zuwa.

Hare-haren na Amurka sun tsaya cak kai tsaye kan Iran ko kuma manyan jagororin dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Quds Force a cikin iyakokinta, yayin da Amurka ke kokarin hana rikicin daga ci gaba da ruruwa. Sai dai Iran din ta musanta zargin da aka yi mata akan kai harin na Jordan.

Koda shike dai Ba a san irin tasirin da wannan harin na Amurka zai yi ba.

Ko da yake daya daga cikin manyan mayakan sa-kai da Iran ke marawa baya, Kataib Hezbollah, ya ce yana dakatar da kai hare-hare kan sojojin Amurka, wasu kuma sun sha alwashin ci gaba da fafatawa, suna mai da kansu a matsayin masu fafutukar kare hakkin Falasdinu yayin da yakin Gaza ke nuna babu alamar kawo karshe.

Mai magana da yawun kwamitin tsaron kasar John Kirby ya ce an zabo wuraren a tsanake domin kaucewa hasarar fararen hula kuma bisa kwararan hujjoji da ba za a iya musantawa ba da ke nuna cewa suna da alaka da harin da aka kai kan jami'an Amurka a yankin.

Kirby dai Ya ki yin cikakken bayani game da cikakkiyar shaidar da kuma sahihancinta.

Laftanar Janar Douglas Sims, darektan rundunar hadin gwiwa ya bayyana cewa an kai hare-haren ne na tsawon kimanin mintuna 30, kuma uku daga cikin wuraren da aka kai harin uku daga ciki sassan na Iraki ne, hudu kuma a Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.