Hukumar EFCC A Najeriya Ta Gurfanar Da Wani Alkali Gaban Kotu Saboda Karban Rashawa
Hukumar yaki da masu halatta kudaden haram a Nigeria, EFCC a takaice ta shigar da kara gaban babbar kotun Lagos don neman a gurfanar da wani alkali James Agbadu-Fishim na kotun sasanta rikicin ma'aikata saboda karban cin hanci na kudaden da suka kai Naira miliyan uku da dubu dari biyar.
Wallafawa ranar:
Kamar yadda takardan shigar da karar ke nunawa ana zargin alkalin ya karbi wadannan kudaden cin hanci ne daga hannun wani babban Lauya dake zaune a Lagos tsakanin shekara ta 2013 da shekara ta 2015.
A cewar EFCC suna da takardun shigar da wadannan kudade cikin asusun bankin wannan Alkali.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu