Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya: Fursunoni 36 sun tsere daga gidan yari

Gwamnatin Najeriya tace an hallaka fursunoni 4, yayinda wasu 36 suka tsere daga gidan yarin Jihar Akwa Ibom, bayan arangamar da suka yi da jami’an dake kula da su.

Ma'aikatan gidan yari suna fuskantar barazanar bore lokaci zuwa lokaci.
Ma'aikatan gidan yari suna fuskantar barazanar bore lokaci zuwa lokaci. The News Nigeria
Talla

Bayanai sun ce ‘yan gidan yarin sun yi amfani da wasu adduna da suka kwace a inda ake dafa musu abinci, wajen kai hari kan masu kula da su, abinda ya haifar da arangama a tsakanin bangarorin biyu.

Alex Oditah, Babban jami’in dake kula da gidan yarin a Jihar ta Akwa Ibom, yace an kaddamar da bincike kan lamarin, kuma tuni aka kama 7 daga cikin wadanda suka tsere, yayinda jami’an tsaro ke ci gaba da farautar ragowar fursunoni 36.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.