Canada zata tallafa wa Najeriya da dala miliyan 10 saboda tsaro
Kasar Canada zata baiwa Najeriya dala miliyan goma amatsayin tallafawa gwamnati wajen yaki da matsalolin tsaro.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Jakadan Canada mai rikon kwarya a Najeriya Nicholas Simard bayyana bada wannan tallafiya, yayin da ya ziyarci ministan ‘yan sandan kasar Muhammad Maigari Dingyadi a Abuja, inda ya jaddada bukatar inganta karfin jami'an' yan sanda, da sauran abubuwa don rage tashin hankali da kasar ke fuskanta.
Shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na Ma’aikatar Harkokin ’Yan sanda, Odutayo Oluseyi, a cikin wata sanarwa a karshen mako, ya ruwaito Simard yana cewa Najeriya kasa ce mai ci gaba ta fuskoki da dama, to amma rashin tsaro na neman zama babban kalubale ga ci gabanta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu