Isa ga babban shafi
RIGAKAFIN-YARA

Majalisar Dinkin Duniya tayi gargadi kan kasa yiwa yara rigakafi

Majalisar Dinkin Duniya tayi gargadin cewar duniya na fuskantar babbar barazana sakamakon kasa gabatar da allurar rigakafin da aka saba yiwa kananan yara saboda annobar korona, inda tace miliyoyin yaran na fuskantar yiwuwar kamuwa da cutar kyanda da wasu cututtuka na daban.

Shugaban Hukumar Lafiya Tedros Adhanom Gebreyesus
Shugaban Hukumar Lafiya Tedros Adhanom Gebreyesus © KEYSTONE/MARTIAL TREZZINI sda-ats
Talla

Alkaluman Hukumar Lafiyar da na Hukumar kula da kananan yara ta UNICEF sun nuna cewar yara miliyan 23 suka kasa samun allurar rigakafin bara, sakamakon yadda annobar korona ta mamaye duniya.

Wannan shine adadi mafi yawa da aka taba gani a cikin shekaru 10, wanda kuma ya dara na shekarar 2019 da yara miliyan 3 da dubu 700.

Daga cikin wadanda basu karbi rigakafin bara ba harda yara miliyan 17 dake zama a yankunan da ake fama da tashe tashen hankula ko kuma masu zama a unguwannin marasa galihu a birane.

Babbar jami’ar kula da sashen rigakafi ta Hukumar Lafiya Kate O’Brien ta bayyana cewar ana fuskantar babbar matsala a wannan shekara ta 2021 saboda illar dake iya biyo bayan rashin karbar rigakafin.

Jami’ar ta bukaci daukar matakan gaggawa domin shawo kan matsalar wadda ke iya yin illa ga lafiyar kananan yara da kuma al’umma baki daya.

Ita ma shugabar UNICEF Henrietta Fore tace annobar korona ta haifar da matsala sosai dangane da shirin yiwa yara allurar rigakafin, inda take gargadin cewar abinda zai biyo baya kan iya haifar da rasa rayuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.