Isa ga babban shafi
Najeriya - Dangote

Buhari ya jagoranci kaddamar da kamfanin takin zamani na Dangote a Lagos

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jagoranci kaddamar da ma’aikatar samar da takin zamani da ke cikin katafariyar matatar man fetur mallakin attajiirin Afrika Aliko Dangote a jihar Lagos dake kudancin kasar, matatar da ke matsayin irinta ta farko kuma mafi girma a nahiyar Afrika, wadda aka kashewa tsabar kudi dala biliyan 2 da rabi, da kuma ake sa ran ta samar da taki tan miliyan 3 duk shekara.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da wasu mukarrabansa da kuma Alh. Aliko Dangote, shugaban kamfanin Dangote yayin kaddamar da kamfanin Takin Dangote a birnin Lagos, 22/03/22
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da wasu mukarrabansa da kuma Alh. Aliko Dangote, shugaban kamfanin Dangote yayin kaddamar da kamfanin Takin Dangote a birnin Lagos, 22/03/22 © Bashir Ahmad
Talla

Baya ga sashen samar da takin zamanin, sashen matatar man fetur da ake saran ya fara aiki shima dai cikin shekarar nan za ta rika samar da ganga dubu 650 kowacce rana.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da wasu mukarrabansa da kuma Alh. Aliko Dangote, shugaban kamfanin Dangote yayin kaddamar da kamfanin Takin Dangote a birnin Lagos, 22/03/22
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da wasu mukarrabansa da kuma Alh. Aliko Dangote, shugaban kamfanin Dangote yayin kaddamar da kamfanin Takin Dangote a birnin Lagos, 22/03/22 © Bashir Ahmad

Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya yaba da tsarin samar da wannan makamashi da shaka babu zai taimaka wajen samar da guraban ayukan yi a kasar da sake farfado da tattalin arzikin Najeriya.

Hamshakin attajirin Afirka Alh. Aliko Dangote, cikin kamfanin sa na Taki a Lekki dake Lagos
Hamshakin attajirin Afirka Alh. Aliko Dangote, cikin kamfanin sa na Taki a Lekki dake Lagos © Bashir Ahmad

A wannan bikin da ya gudana a Lagas,an samu halartar gwamnoni,sarakunan gargajiya da wakilan jama'a.

Shugaban Najeriya Buhari ya jaddada goyan bayan sa ga ayukan samar da wannan makamashi daga cikin gida zuwa kasashen waje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.