Isa ga babban shafi

Sojin ruwan Najeriya sun dakile safarar haramtattun kayayyaki a Niger Delta

Rundunar sojin ruwan Najeriya ta kama wasu mutane da dama tare da haramtattun kayayyakin da suke safarar su, wadanda darajar kudinsu ta kai sama da dalar Amurka 700,000.

Sojojin ruwan Najeriya yayin sintiri a mashigar ruwan tekun Guinea.
Sojojin ruwan Najeriya yayin sintiri a mashigar ruwan tekun Guinea. © AP Photo/Sunday Alamba
Talla

Sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin Najeriyar ya fitar Comodore Adedotun Ayo-Vaughan ta ce rundunar ta ta musamman mai suna ‘Operation Dakatar Da Barawo’ wato ‘OPDDB’ ce ta samu nasarar kamen miyagun da kuma haratattun kayayyakin da suke safara, a yankunan da ake hako mai na Najeriya.

Tun a ranar 1 ga watan Afrilun nan aka kaddamar da rundunar ta ‘Operation Dakatar da Barawo’ don dakile mummunar satar albarkatun man da ake kuntukawa Najeriya.

A cikin watan Maris hukumar kula da harkokin man fetur ta Najeriya, ta ce kasar ta yi asarar fiye da dala biliyan 3 na mai, wanda aka sace cikin watanni 14 da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.