Isa ga babban shafi

Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 50 a jihar Jigawa ta arewacin Najeriya

Wasu alkaluman hukumar agaji ta Najeriya sun tabbatar da mutuwar akalla mutane 50 sakamakon ambaliyar ruwan da yankin arewacin kasar ya fuskanta biyo bayan kakkarfan ruwan saman da ake ci gaba da samu tun daga watan Yuni zuwa yanzu.

Wani yanki na Jihar Jigawa a Najeriya da ya fuskanci ambaliyar ruwa.
Wani yanki na Jihar Jigawa a Najeriya da ya fuskanci ambaliyar ruwa. Premium Times Nigeria
Talla

Hukumar agajin gaggawa ta jihar jigawa SEMA, ta ce duk da kasancewar jihar a sahun wadanda ke fuskantar ibtila’in ambaliyar kowacce shekara, a wannan karon lamarin ya tsananta fiye yadda masana suka yi hasashe.

Shugaban hukumar ta SEMA, Yusuf Sani ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP cewa ambaliyar ta faru a kananan hukumomin jihar 27 kuma zuwa yanzu akwai alkaluman mutum 50 da aka tabbatar sun mutu sanadiyyar ambaliyar.  

Yusuf Sani ya ce kwanaki 3 na karshen makon da ya gabata, su suka kasance mafiya tayar da hankali ta yadda aka ga zubar ruwan sama babu kakkautawa a cikinsu.

Shugaban hukumar ta SEMA ya ce zuwa yanzu sun kirge dubunnan mutane wadanda ibtila’in ya shafa kuma sun cikin halin bukatar agajin gaggawa.

Karamar hukumar Kafin Hausa na matsayin yankin da matsalar ta ambaliyar ruwa ta fi yiwa barna inda ta kashe mutane 10 sai wasu 68 da ke kwance a asibitoci kana ta raba wasu mutane dubu 1 da 436 da muhallansu galibi daga kauyen Balangu da ambaliyar ta rushe gidaje 237.

 Zuwa yanzu jihar ta jigawa ta samar da matsugunan wucin gadi 11 don killace wadanda ambaliyar ta shafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.