Isa ga babban shafi

Birtaniya za ta bai wa Najeriya fam miliyan 95 don bunkasa noma

Birtaniya za ta baiwa Najeriya tallafin Fam miliyan 95 a wani yunkuri na taimakawa kasar don bunkasa tsarin noman da zai jurewa tasirin matsalolin sauyin yanayi a kasar, matakin da ke zuwa dai dai lokacin da tuni manoman kasar ta yammacin Afrika suka fara ganin tasirin dumamar yanayi ga amfanin gonar da suke shirin girbewa a damunar bana.

Wani manomi a Najeriya.
Wani manomi a Najeriya. Fati Abubakar/RFI
Talla

Sakataren harkokin wajen Birtaniya, James Cleverly, da ke jawabi kan wannan tsari a gaban taron sauyin yanayi na bana wato COP27 da ke gudana a Masar ya ce akalla ‘yan Najeriya miliyan 4, ciki har da mata miliyan 2 ne za su ci gajiyar wannan tallafi don bunkasa sana’arsu ta noma da nufin samar da tsarin noman na zamani da zai jurewa tasirin matsalolin sauyin yanayi, a yayinda a gefe guda kuma ya rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli.

Gwamantin Birtaniya ta sabunta aniyar tata ce a yayin da ta ke sanar da kari a kasafin kudi na shirin yaki da sauyin yanayi zuwa Fam biliyan 1 da rabi a shekarar 2025.

Cleverly ya ce kasarsa za ta bai wa nahiyar Afrika fifiko a shirinta na taimakawa muhalli, inda ya kara da cewa ta shiga hadaka da bankin bunkasa nahiyar Afrika don samar da wata sabuwar kafa da za a samu kudaden ririta yanayi wadda za ta ci gajiyarta.

A waje daya kuma, magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya yi kira ga shugabannin kasashen duniya su ribanya kokarinsu wajen bunkasa tsarin da aka shimfida na yakar sauyin yanayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.