Isa ga babban shafi

Za mu yi amfani da karfi don murkushe masu shirin kawo tarnaki ga zabe- Sojoji

Shugabannin Sojojin Najeriya sun ce za su yi amfani da karfin da ya wuce kima akan mutanen da ke shirin lalata zaben shugaban kasar da za a yi a karshen wannan mako. 

Manjo Janar Farouk Yahaya, babban hafsan sojin Najeriya.
Manjo Janar Farouk Yahaya, babban hafsan sojin Najeriya. © NIgerian Army
Talla

Daraktan yada labaran ma’aikatar tsaron kasar, Janar Tukur Gusau ya bayyana haka yayin bayani ga manema labarai a kan shirin da sojojin suka yi domin tabbatar da tsaron kasa lokacin zabubbukan da za a yi. 

Wannan matsayi na zuwa kwana guda bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci taron majalisar tsaron kasa wanda ya karbi rahotanni daga hafsoshin hukumomin tsaron kasar akan halin da ake ciki. 

Shugabannin hukumomin sun tabbatarwa shugaban kasar cewar jami’ansu na cikin damara domin samar da tsaron da ake bukata wajen ganin an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali. 

Bayan taron Sufeto Janar na 'yan sanda Alkali Baba yace shugaba Buhari ya basu umurnin daukar duk matakan da suka dace wajen ganin an murkushe duk wani yunkuri na yiwa zaben zagon kasa. 

Rahotanni daga yankunan kasar na nuna cewar ana ci gaba da girke jami’an tsaron cikin shirin ko ta kwana domin samar da tsaro ga ma’aikatan zabe da kuma jama’a baki daya. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.