Isa ga babban shafi

Masu hidimar kasa sun janye daga aikin zabe saboda barazanar tsaro

Masu aikin hidimar kasa fiye da 100 ne yanzu haka suka janye daga shiga aikin zaben shugaban kasa a jihar Imo ta kudancin Najeriya, sabodar fargabar abin da ka je ya zo lura da tashe-tashen hankulan da ake gani a jihar.

Wasu masu aikin hidimar kasa a Najaeriya.
Wasu masu aikin hidimar kasa a Najaeriya. © rfi
Talla

Kwamishinar hukumar zabe ta jihar Sylvia Agu ta ce sai a jiya alhamis ne suka samu sanarwar janyewar jami’an na NYSC daga aikin zaben musamman wadanda aka tura kananan hukumomin Okigwe da Orlu da Orsu yankunan da ake ganin tsanantar hare-haren ‘yan bindiga.

Wannan mataki na zuwa ne a dai dai lokacin da hadakar jami’an tsaron Najeriya da suka kunshi Sojoji da ‘yan sanda da kuma DSS suka fara wani sumame na musamman kan maboyar batagari da sauran ‘yan daba a jihohin kasar a wani yunkuri na kame don dakile illar da suke shirin yiwa zaben na gobe asabar.

Ko a jihar Kano an ga yadda jami'an tsaro suka kame 'yan daba akalla 63 bayan wata arangama tsakaninsu da magoya bayan jam'iyyar NNPP da rahotanni ke cewa an kashe mutane hudu tare da kone tarin motoci.

Babban sufeton 'yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba ya sha alwashin murkushe duk wata barazanar tsaro da ka iya tasowa yayin zaben, sai dai har yanzu mutane na zaman dar-dar saboda hare-haren da ake gani a wasu sassan Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.