Isa ga babban shafi

Manyan kasashe na kiraye-kirayen bukatar gudanar da sahihin zabe a Najeriya

Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen Turai da Amurka da Birtaniya da Canada da Japan da Australia da Norway sun gabatar da sanarwar hadin gwiwa inda su ke bukatar shugabannin Najeriya da su tabbatar da ganin an gudanar da karbaben zabe cikin kwanciyar hankali a karshen wannan mako. 

Wani jami'in hukumar zaben Najeriya, yayin kidayar kuri'u
Wani jami'in hukumar zaben Najeriya, yayin kidayar kuri'u REUTERS/Adelaja Temilade
Talla

Sanarwar ta ce ya na da muhimmanci ga zaman lafiyar Najeriya da kuma ci gaban dimokradiyyar ta a gudanar da zaben cikin lumana domin tabbatar da sahihancinsa. 

Kasashen sun bukaci duk masu ruwa da tsaki a kasar da su bada gudumawa wajen ganin an kwantar da hankalin jama’a da kuma kaucewa tashin hankali. 

Sau tari akan samu matsalolin tashin hankali a wasu sassan Najeriya lokacin gudanar da zabe, sakamakon yadda wasu batagarin ‘yan siyasa ke tinzira jama’a ko kuma magoya bayansu. 

'Yan takara 18 dake fafatawa a zaben wannan shekarar sun rattaba hannu a yarjejeniyar zaman lafiya domin janyo hankalin magoya bayansu da su kaucewa tarzoma ko kuma tashin hankali kafin zaben da lokacin da ake gudanar da shi da kuma bayan zaben. 

Shugaban Najeriya mai baring ado, Muhammadu Buhari ya roki ‘yan takarar da mutunta dokokin zaben da aka gindaya domin kaucewa jefa kasar cikin tashin hankali. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.