Isa ga babban shafi

INEC ta dage zaben gwamnonin Najeriya

Hukumar Zaben Najeriya ta INEC ta dage zaben gwamnonin jihohin kasar da mako guda, inda yanzu za ta gudanar da zaben a ranar 18 ga watan nan na Maris a maimakon 11 ga watan da aka sanar tun da fari.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu REUTERS - REUTERS TV
Talla

INEC ta ce, tana bukatar karin lokaci domin sake saita na'urar BVAS wadda ta yi amfani da ita a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabairu da ya gabata.

Yanzu haka 'yan takara za su iya ci gaba da yakin neman zaben su har zuwa tsakar daren ranar 16 ga watan Maris, wato sa'o'i 24 gabanin kada kuri'a a zabukan na gwamnoni da 'yan majalisar jihohin.

A ranar Laraba ne, kotun daukaka kara a Najeriya ta bai wa INEC umarnin ta sake saita na'urar ta BVAS, cikin shirye-shiryenta na gudanar da zabukan na gwamnoni da 'yan majalisar jihohi.

Umarnin kotun na zuwa ne bayan 'yan takarar shugabancin Najeriya, Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP da Peter Obi na jam'iyyar Labour  Party sun nemi a ba su damar gudanar da binciken kwa-kwaf cikin na'urar ta BVAS bayan sun yi zargin cewa, an yi musu magudi.

Wani jami'in zabe na amfani da na'urar BVAS domin tantance wani mutun da ke shirin kada kuri'arsa. 2023/02/25.
Wani jami'in zabe na amfani da na'urar BVAS domin tantance wani mutun da ke shirin kada kuri'arsa. 2023/02/25. AP - Mosa'ab Elshamy

A karon farko kenan da Hukumar Zaben Mai Zaman Kanta ta INEC ke amfani da na'urar tantance masu kada kuri'a ta BVAS a zaben shugaban kasa da ya gudana, tana mai cewa, na'urar na da muhimmanci kwarai wajen dakile magudin zabe a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.