Isa ga babban shafi

Zaben Najeriya: Kakakin majalisar dokokin Yobe ya sha kaye gun wani matashi

Kakakin majalisar dokokin jihar Yobe  a Najeriya, Ahmed Mirwa Lawan mai wakiltar mazabar Nguru II a majalisar dokokin jihar,  ya rasa kujerarsa ta dan majalisar, bayan da wani matashi mai shekaru 35, dan jam’iyyar PDP ya kayar da shi a zaben da ya gudana a Asabar din nan.

Akwatunan zabe na Tarayyar Najeriya.
Akwatunan zabe na Tarayyar Najeriya. REUTERS/Luc Gnago
Talla

Babban jami’in zabe na jihar ta Yobe,Dokta Habib Muhammad, wanda ya sanar da sakamakon, ya ce Musa ya lashe kuri’u 6,648, inda ya doke kakakin majalisar dokokin jihar, dan jam’iyyar APC wanda ya samu kuri’u  6,466 votes.

Ya ce saura ‘yan takarar na jam’iyyun ADC, NNPP APM sun ci 3,023 da 14 kowanne.

Kakakin majalisar dokokin jihar Yoben da ya sha kasa, ya kasance dan majalisar dokokin jihar tun daga shekarar 2003, a lokacin da aka zabe shi a karkashin jaam’iyyar ANPP.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.