Isa ga babban shafi

Bilbis ya lashe kujerar Majalisar Dattawan Zamfara ta tsakiya

Tsohon ministan yada labaran Najeriya, Ikra Aliyu Bilbis ya lashe zaben kujerar Majalisar Dattawan Zamfara ta tsakiya sakamakon nasarar da ya samu a zaben da aka kammala a karshen makon da ya gabata.

Tsohon ministan yada labaran Najeriya, Ikra Aliyu Bilbis tare da magoya bayansa.
Tsohon ministan yada labaran Najeriya, Ikra Aliyu Bilbis tare da magoya bayansa. © Facebook/Ikra Aliyu Bilbis
Talla

Hukumar zaben Najeriya tace Bilbis daga Jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 102,866 abinda ya bashi nasara akan tsohon Sanatan da ya wakilci yankin Kabiru Marafa na jam’iyyar APC wanda ya samu kuri’u 91,216. 

Zababben Sanatan ya jinjinawa mutanen Zamfara ta tsakiya saboda karimcin da suka masa wajen sanya shi a gaba ya wakilce su a majalisar dattawa, yayin da ya bayyana cewar ba zai yi kasa a gwuiwa ba wajen gabatar musu da wakilci mai inganci wanda za’a dinga basu damar gabatar da bukatun su a koda yaushe a zauren majalisa. 

Bilbis yace batun zabe ya kare, yanzu kowa na shi ne a mazabar Zamfara ta Tsakiya, kuma zai yi dukkan abinda ya dace domin ganin kowa yaci gajiyar wakilcinsa a majalisar dattawa ta kasa. 

Shima Sanata Kabiru Marafa wanda ya amsa shan kaye a zaben ya kuma mika godiya ga daukacin mutanen mazabarsa saboda karimcin da suka masa a baya wajen bashi damar wakiltar su a matakai daban daban. 

Marafa yace bukatarsa itace ci gaba da yiwa mazabarsa da jihar Zamfara aiki, kuma tunda haka Allah ya sa sakamakon ya kasance ya rungumi kaddara kuma zai ci gaba da yi musu hidima ta wata hanya ta daban, yayin da ya bayyana cewar ba zai je kotu domin kalubalantar sakamakon zaben ba. 

Wannan nasara ta Ikra Bilbis da Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ta sanya Jam’iyar PDP ta samu kujeru 36 a Majalisar Dattawa, yayin da APC ke ci gaba da rinjaye da kujeru 59 cikin su harda wanda Sanata Aliyu Magatakarda Wammako ya samu a karshen mako. 

Sakamakon zabukan sun nuna cewar jam’iyyar LP na da kujeru 8 sai kuma NNPP da SDP da kujeru bibbiyu. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.