Isa ga babban shafi

Manoma a Najeriya na korafi game da tsadar takin zamani

Manoman Najeriya na kokawa a kan hau hauhawar farashin takin noma, duk da samun yawaitar masu sarrafa shi a kasar.

Des ouvriers remplissent des sacs d'engrais dans l'usine Elephant Vert de la zone industrielle «Agropolis» à Meknès, dans le nord du Maroc, le 9 décembre 2021
Des ouvriers remplissent des sacs d'engrais dans l'usine Elephant Vert de la zone industrielle «Agropolis» à Meknès, dans le nord du Maroc, le 9 décembre 2021 AFP - FADEL SENNA
Talla

Farashin takin noman na karuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin kasar ta zuba sama da Dala miliyan 121 a wani Shirinta na  samar da wadataccen taki.

Najeriya da ke da yawan manoman shinkafa da rake,yawancinsu tsadar taki ya haifar musu da matsaloli mabambanta wajen samun adadin da suke bukata na takin da za su yi amfani da shi wajen noma.

Yayin da wata manomiya Ajulo Mojisola ta ce wani bangare na gonarta  ne kawai ta iya nomawa, saboda tsadar takin zamani.

Mojisola ta cigaba da cewa ta rage girman gonar ta ne saboda bazata iya siyan adadin takin da take bukata ba sabida tsadar sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.