Najeriya: Kotuna sun raba 'yan majalisan Tarayya 31 da kujerun su kawo yanzu
Kotunan da ke sauraron shari’ar zabe a Najeriya sun gabatar da hukunce hukunce daban daban a baya-bayan nan wadanda suka raba ‘yan majalisun tarayya 31 da kujerun su.
Wallafawa ranar:
Daga cikin mazabun da aka soke wadannan zabukan ‘yan majalisun tarayya, akwai mazabun Kogi ta Gabas da Kogi ta Tsakiya, sai kuma Delta ta Tsakiya da Delta ta Kudu tare da kujerar Filato ta kudu.
Yayin da kotu ta bukaci gudanar da zabuka a wasu yankuna na kujerun Kogi ta Gabas da Delta ta Kudu da kuma Delta ta Tsakiya, kotun ta kuma mikawa ministan kwadago Simon Bako Lalong kujerar Sanatan Filato ta Kudu.
Ga jerin ‘yan majalisun wakilan da suka rasa kujerun su da kuma jam’iyyun da suka fito:
Umar Ysuuf Datti – NNPP, Kano
Amobi Ogah – LP , Abia
Fred Agbedi – PDP, Bayelsa
Ngozie Okolie – LP, Delta
Umar Yerima – NNPP, Kano
Ikenga Ugochinyere – PDP, Imo
Chijioke Okereke – LP, Enugu
Seyoi Sowunmi – LP, Lagos
Aminu Chindo – PDP, Katsina
Ismaila Dalha – PDP, Katsina
Peter Gyandeng – PDP, Filato
Munachim Alozie – LP, Abia
Ibe Osunwa – LP, Abia
Francis Waive – APC, Delta
Joshua Gana – PDP, Niger
Emeka Nnamani – LP, Abia
Jonathan Ukodhiko – PDP, Delta
Idris Dankawa NNPP, Kano
Adamu Yakubu – NNPP, Jigawa
Thaddeus Atta – LP, Lagos
Dachung Musa Bagos – PDP,Filato
Beni Lar – PDP, Filato
Sunday Umeha – LP, Enugu
Mohammed Jamilu – PDP, Katsina
Ilyasu Abubakar – PDP, Katsina
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu