Isa ga babban shafi

An fara zaman yanke hukuncin karshe kan zaben shugaban Najeriya

Kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa (PEPT) na zaman yanke hukunci a yau, yayin da aka tsaurara matakan tsaro gabanin yanke hukunci a ciki da wajen kotun.

Atiku Abubakar da kuma Peter Obi su ke kan gaba wajen kalubalantar sakamakon zaben, inda su ke neman a soke zaben, saboda zargin an tafka magudi.
Atiku Abubakar da kuma Peter Obi su ke kan gaba wajen kalubalantar sakamakon zaben, inda su ke neman a soke zaben, saboda zargin an tafka magudi. © Daily Trust
Talla

‘Yan Najeriya daga sassa daban-daban na zaman jiran ganin yadda ake gudanar da shari’ar kai tsaye ta gidan talabijin daga harabar kotun daukaka kara da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da Peter Obi na jam’iyyar Labour LP da kuma jam’iyyar APM su ne suka shigar da kara suna kalubalantar nasarar shugaba Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2023.

Jiga-jigan 'yan siyasa

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da jiga-jigan jam'iyyar Labour (LP) da gwamnoni da jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulki, da na PDP na harabar kotun don sauraron yadda za ta kaya.

Sauran gwamnonin APC da suka halarci zaman har da na Kogi, Yahaya Bello; da Abdullahi Sule na Nassarawa da na Imo, Hope Uzodimma;  sai na Ekiti, Biodun Oyebanji; da kuma na Yobe Mai Mala Buni.

Shugaban APC na kasa Abdullahi Ganduje; da Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu duk sun hallara.

PDP

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi yana cikin manyan jiga-jigan jam'iyyar PDP da suka halarci zaman kotun a Abuja.

Julius Abure na jam’iyyar LP da mai magana da yawun yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar Yunusa Tanko na daga cikin wasu jiga-jiga da ke zaune a zauren kotun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.