Isa ga babban shafi

Mashakon Diphtheria ya kashe mutane 10 cikin 91 da suka harbu a Jigawa

Ma’aikatar lafiya ta jihar Jigawa a Najeriya, ta tabbatar da barkewar annobar mashakon Diphtheria da zuwa yanzu ya kashe mutane 10 cikin 91 da suka harbu.

Wani yaro yayin karbar rigakafi.
Wani yaro yayin karbar rigakafi. AP - Thoko Chikondi
Talla

Babban sakataren ma’aikatar lafiya na jihar Dr Salisu Mu’azu yayin jawabinsa gaban manema labarai jiya juma’a a birnin Dutse ya ce annobar cutar ta Diphtheria ta fantsama a kananan hukumomin Kazaure da Jahun.

A cewar jami’in tuni aka aike da samfurin mutane da dama da ake zaton sun harbu da cutar don gudanar da cikakken gwaji a Abuja.

Babban sakataren ya bayyana cewa yankunan da cutar ta fi tsananta, yankuna ne da aka samu karancin alluran rigakafin cutuka ga kananan yara.

A cewar Dr Salisu, gwamnatin jihar ta Jigawa ta dauki matakan rigakafi ga yankuna da dama tun bayan tsanantar cutar ta Diphtheria a jihohin Kano da Yobe da ke makwabtaka da ita.  

Dr Salisu Mu’azu ya ce yanzu haka suna dakon isowar alluran rigakafin cutar don bayar da matakan kariya ga al’umma musamman a yankunan da aka samu bullarta.

Alkaluma sun nuna cewa galibin wadanda suka harbu da cutar ta Diphtheria kananan yara ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.