Isa ga babban shafi

Jarumin fina finan Nollywood Mr Ibu ya rasa kafarsa sakamakon rashin lafiya

Afirka – Daya daga cikin fitattun jaruman shirin fina finan Najeriya a masana’antar Nollywood, John Okafor da aka fi sani da suna ‘Mr Ibu’, ya rasa kafarsa sakamakon cutar siga wadda ta sanya likitoci yanke ta domin ceto rayuwarsa.

John Okafor
John Okafor © @Premium Times
Talla

Kasa da wata guda bayan da jarumin ya aike da sako ga jama’ar Najeriya domin ceto lafiyarsa daga barazanar rasa kafar, yanzu ta tabbata cewar an yanke ta a asibiti.

A wancan sakon bidiyon da ya aike, Mr Ibu ya nemi taimako da kuma addu’ar ‘yan Najeriya na ceto rayuwarsa, inda yake cewa baya bukatar ganin an kaiga yanke kafar kamar yadda likitoci suka bada shawara.

Sai dai a litinin din nan, Mr Ibu ya sake gabatar da wata sanarwar dake cewar yanzu ta tabbata an yanke masa kafar.

Rahotanni sun ce iyalan gwarzon fina finan ne suka gabatar da sanarwar dake cewa da misalin karfe 1 na ranar litinin aka yankewa mahaifinsu kafa bayan wasu ayyuka guda 7 da likitoci suka masa domin ceto rayuwarsa.

Iyalan sun ce matakin ya girgiza su, amma ya zama wajibi su hakura da aikin domin ceto rayuwarsa.

Daga nan sai suka aike da sakon godiya ga daukacin wadanda suka taimaka musu wajen ceto rayuwar mahaifin na su, yayin da suka ce Mr Ibu da kansa zai gabatar da na shi godiyar nan gaba.

Daga cikin wadanda suka kaiwa jarumin fina finan dauki akwai Gidauniyar tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki wadda tace ta biya daukacin kudaden da ake bukata na jinyar har zuwa ranar 18 ga watan Oktobar da ta gabata.

Mr Ibu na daya daga cikin fitattun jaruman fina finan Nollywood, kuma ya fito a fim sama da 200 da aka nada.

Duk da gudumawar da masu sana’ar fina finai ke bayarwa a Najeriya, har yanzu babu wani ingantaccen shiri na kula da rayuwarsu da kuma makomarsu idan sun yi ritaya daga aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.