Isa ga babban shafi
ZABEN GWAMNA

Kotun daukaka kara ta tabbatar da zaben gwamna Inuwa Yahya na Gombe

Najeriya – Kotun daukaka kara a Najeriya ta tabbatar da zaben gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahya na jam’iyyar APC, yayin da tayi watsi da kalubalantar nasarar sa da jam’iyyar PDP da kuma ADC suka yi a gaban ta

Gombe Governor Inuwa Yahaya
Gombe Governor Inuwa Yahaya © RFI Hausa
Talla

Mai shari’a Orji Abadua ya jagoranci alkalai guda 3 wajen yanke hukuncin da kuma tabbatar da nasarar Inuwa Yahya a zaben saboda samun kuri’un da yawansu ya kai dubu 342 da 821, kamar yadda hukumar zabe ta INEC ta sanar a watan Maris.

Alkali S.B. Belgore yace jam’iyyun PDP da ADC sun gaza gabatar da hujjojin da zasu tabbatar da zargin magudi da rashin bin ka’ida da su kace anyi a lokacin zaben na gama gari da ya gudana a farkon wannan shekarar.

Hukumar zabe a Najeriya ta sanar da gwamna Yahya a matsayin wanda ya samu nasarar zaben gwamnan Gombe domin yin wa’adi na biyu, sakamakon yawan kuri’un da ya samu, abinda ya sashi a sahun gaba cikin jerin ‘yan takarar da suka shiga zaben.

Jam’iyyar PDP wadda ta tsayar da Jibrin Barde a matsayin dan takararta ce ta zo ta biyu a zaben da ya gabata.

Kotun sauraren zaben da ta zauna a jihar Gombe, ta tabbatar da nasarar Inuwa Yahya na APC, amma jam’iyyun PDP da ADC suka ki amincewa da hukuncin, abinda ya sa suka daukaka kara zuwa matakin babbar kotun da ta yanke hukunci ayau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.