Isa ga babban shafi

Sojin Najeriya sun ceto mutanen da 'yan bindiga suka sace a Kebbi

Sojin Najeriya da taimakon ‘yan sa kai sun yi nasarar ceto akalla mutane 6 da ‘yan bindiga suka sace tare da shiga da su dajin da ke karamar hukumar Shanga ta jihar Kebbi.

'Yan bindiga sun addabi jihohin arewa maso yammacin Najeriya
'Yan bindiga sun addabi jihohin arewa maso yammacin Najeriya © dailypost
Talla

Daraktan tsaro na ofishin gwamnan jihar ta Kebbi Abdulrahman Usman ya shaidawa manema labarai cewa dukkanin mutanen 6 an sada su da iyalansu bayan nasarar ceto su daga hannun ‘yan bindigar.

A cewar Abdulrahman Usman, dakarun runduna ta 1 ta barikin Dukku da ke birnin Kebbi ne suka kai sumamen kan tsaunukan Kogon Damisa da ke Saminaka a karamar hukumar Shanga da ke kan iyakar jihar ta Kebbi da makwabciyarta jihar Niger.

Daraktan tsaron, ya ce yayin sumamen wanda ya gudana da taimakon jami’an sa kai, an yi nasarar kame tarin ‘yan bindiga baya ga ceto mutanen 6 wadanda suka bace tsawon lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.