Matasan Jigawa sun dauki matakin yaki da ambaliyar ruwa
Shekara guda kenan da faruwar mummunar ambiyar ruwa a wasu jihohin Najeriya, kuma jihar Jigawa da ke arewacin kasar na cikin jihohin da ambaliyar ta yi wa barna. Karamar Hukumar Auyo na cikin yankunan da ambaliyar ta shafe baki daya a wancen lokaci, wannan ta sa RFI Hausa ziyartar yankin don ganin matakin da jama’a ke dauka na kariya daga ambaliyar.
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:12
Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken rahoton Abubakar Isa Dandago.
Dimbin matasan garin ne suka fito domin katange yankinsu da zummar dakile kwararowar ambaliyar ruwan a wannan karon.
Garin na Gamahuwai na kan gaba wajen fuskantar bakar azabar ambaliyar a shekarar da ta gabata, inda ruwan ya shafe baki dayan garin tare da awon gaba da komai
Wani abun tausayin ma dai shi ne yadda ambaliyar ta wuce da rayuka kusan 20, baya ga wadanda bakin cikin asarar ya haddasawa cikawa.
Baya ga asarar rayukan da aka samu a wancan lokacin, ambaliyar ta kuma haddasa koma-bayan harkokin kasuwanci da na yau da kullum.
Babban tashin hankalin bai wuce yadda ambaliyar ta maida masu hannu da shuni 'yan rabbana ka wadata mu ba sakamakon dimbin asarar da suka tabka a wancan lokacin.
Wannan dai ita ce mummunar ambaliyar da yankin ya taba fuskanta cikin shekaru sama da 60, a cewar dattijo Malam Hudu guda daga wadanda suka tsallake suka bar iayalansu saboda halin matsin da suka shiga a bara.
Babban abin dubawa dai bai shige azamar mahukunta ba game da lalubo mafutar bala’in na ambaliyar wanda ya zamo tamkar al’ada a galibin yankunan arewacin Najeriya, lura da babbar asarar da take haifarwa
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu