Isa ga babban shafi

Kotun Koli ta tabbatar da Abba Kabir a matsayin zababben gwamnan Kano

Kotun kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Injiniya Abba Kabir Yusuf a zaben gwamnan jihar Kano na bara, shari’ar da ke kawar da hukuncin kotunan sauraren kararrakin zabe da kuma kotun daukaka kara wadanda da farko suka bayyana Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf © Aminiya
Talla

Zaman kotun wanda ya gudana yau Juma’a a Abuja fadar gwamnatin kasar, kotun ta kore dukkanin hujjojin da ken una cewa Abba Kabir Yusuf bai yi nasara a zaben na ranar 18 ga watan Maris din 2023 ba.

Kotuna 3 kenan na gudanar da shari’ar Gwamnan na Kano wanda ya faro daga kotun sauraren kararrakin zabe zuwa kotun daukaka kara kana kotun kolin a yau Juma’a.

Shari’ar na nuna cewa Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP ya kayar da abokin karawarsa na Jam’iyyar APC Nasiru Yusuf Gawuna a zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.