Isa ga babban shafi

Masu sana'ar gini a Najeriya za su fara yajin aiki na kwanaki 3

Najeriya – Masu sana'ar gini a Najeriya sun bayyana shirin fara yajin aiki daga gobe litinin saboda abinda suka kira kin aiwatar da karin albashi daga bangaren wadanda suke yiwa aiki.

Taswiran Najeriya
Taswiran Najeriya AFP
Talla

Wadannan ma'aikata dake yiwa kamfanoni aiki a karkashin kungiyoyi daban daban sun gabatar da sanarwar hadin gwuiwa dangane da aniyar su ta fara yajin a taron manema labarai.

Babban sakataren kungiyar ma'aikatan gini da kafintoci ta kasa. Ibrahim Walama da takwaransa na manyan ma'aikatan gine gine da injiniyoyi, Tony Egbule sun ce an dauki matsayin fara yajin aikin na kwanaki 3 ne wajen taron da suka yi a ranar 25 ga watan Janairu.

Ma'aikatan sun ce shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da karin albashin naira dubu 35 na wucin gadi ga ma'aikata, amma wadanda suke yiwa aiki sun ki yarda a tattauna a kan yadda za'a biya su domin rage radadin cire tallafin man fetur.

Shugabannin wadannan kungiyoyi sun umarci mambobinsu da su tsunduma cikin yajin aikin daga gobe litinin domin janyo hankalin wadanda suke yiwa aikin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.