Isa ga babban shafi
TSADAR RAYUWA

'Yan majalisun Najeriya sun bukaci komawa tsarin mulki na Firaminista

Najeriya – Wasu 'Yan Majalisun sun bukaci kasar da tayi watsi da tsarin mulkin shugaban kasa mai cikakken ikon da ake amfani da shi yanzu haka, domin komawa tsarin mulki irin na Firaminista kamar yadda aka yi a Jamhuriyar ta farko, domin karkata kudaden da ake kashewa wajen yiwa talakawa aiki.

Sir Abubakar Tafawa Balewa, Firaministan Najeriya na farko
Sir Abubakar Tafawa Balewa, Firaministan Najeriya na farko © The Culture Custodian
Talla

'Yan majalisun sun ce ganin yadda ake kashe makudan kudade ba tare da kaukautawa ba wajen tafiyar da tsarin shugaban kasar da ake amfani da shi yanzu, wanda ke lakume biliyoyin nairorin da ya dace a yiwa talakawa aiki da su wajen harkar bada ilimi da kula da lafiya da kuma yadda ake hana kasa ci gaba, kana da kuma irin karfin fada ajin da bangaren zartawar ke da shi, da wadanda yake nadawa a mukamai daban daban, ya dace a sake nazari domin samarwa kasar mafita.

Tafawa Balewa da Awolowo da Nnamdi Azikwe tsoffin Shugabannin Najeriya a Jamhuriyyar ta Farko
Tafawa Balewa da Awolowo da Nnamdi Azikwe tsoffin Shugabannin Najeriya a Jamhuriyyar ta Farko sunnews

Mai magana da yawun wadannan 'yan majalisar wakilai 60 da suka gabatar da bukatar a shirin yiwa kundin tsarin mulki garambawul, Hon Abdulsamad Dasuki yace suna matukar damuwa da irin makudan kudaden dake tafiya bangaren zartarwar da kuma karfin fada ajin da shugaban kasa mai cikakken iko ke da shi a karkashin wannan tsarin.

Dasuki yace a baya duk kokarin da majalisun tarayya suka yi wajen rage kudaden da ake kashewa bangaren shugaban kasar da kuma ragewa shugaban karfin fada aji ya ci tura saboda masu cin gajiyar tsarin.

Dan majalisar yace duk da yake wannan gyara ne da zai dauki dogon lokaci da kuma bukatar fadakar da jama'ar kasa domin goyan bayan tsarin, suna da yakinin cewar koda ba'a samu biyan bukata a karkashin wannan majalisa ba, ana iya samu a majalisar da zata biyo bayan ta.

Majalisar dokokin Najeriya
Majalisar dokokin Najeriya © AFP - KOLA SULAIMON

A karkashin tsarin mulkin Firaminista da aka yi amfani da shi a Jamhuriya ta farko, bangaren zartarwa na samun karfi ne daga bangaren majalisar dokoki, inda ake zabo firaminista da kuma ministocin sa daga majalisar, matakin dake takaita kashe makudan kudade wajen fadar shugaban kasa da kuma ministocin sa.

Masana na kallon wannan yunkurin a matsayin wanda majalisar ke bukatar aiwatar da ita bayan kammala wa'adi biyu na shekaru 8 na shugaban kasa mai ci, Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2031.

Sir Abubakar Tafawa Balewa ne firaministan Najeriya na farko da ya karbi mulki daga turawan mulkin mallaka lokacin samun 'yancin kai, kafin sojoji su hambarar da gwamnatin sa da kuma hallaka shi, yayin da suka sake dora kasar a karkashin tsarin gwamnati irin na Amurka mai dauke da shugaban kasa.

Rahotanni sun ce 'yan majalisun da suka rattaba hannu a kan wannan bukata sun fito daga daukacin jam'iyyun dake majalisar, ciki harda jam'iyyar APC mai mulki da kuma PDP, babbar 'yan adawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.