Isa ga babban shafi
CAN 2013

‘Yan wasan Mena na Nijar sun ce za su taka rawar gani a Afrika ta Kudu

A bara ne Nijar ta fara shiga gasar cin kofin Afrika da aka gudanar a Gabon da Equatorial Guinea bayan kwashe shekaru ana gudanar da gasar. Amma Nijar ta fice gasar ne a 2012 tun a karon farko ba tare da samun nasarar lashe ko da wasa daya ba.

'Yan wasan Mena na Jamhuriyyar Nijar
'Yan wasan Mena na Jamhuriyyar Nijar AFP PHOTO / ISSOUF SANOGO
Talla

A bana kuma an hada ‘Yan wasan Mena ne a rukuni daya da kasar Ghana da Mali da kuma Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo.

Wasu dai suna ganin a bara Nijar ta samu matsala ne saboda hada mai horar da ‘yan wasan na Mena Harouna Doula da Baturen Faransa bayan Doula ya karbi kyatar Gwarzon koci na hukumar CAF.

Kafin fara wasannin neman shiga gasar ne a bana Rolland Courbis ya ajiye aikin horar da ‘yan wasan Mena kuma a bana dan kasar Jamus ne Gernot Rohr zai jagoranci ‘Yan wasan a Afrika ta Kudu.

Cikin tawagar Mena dai akwai ‘Yan wasa irinsu Mohammed Chikoto da Issoufou Garba da Musa Muazu wadanda za su nemi zira wa kasar kwallaye a raga.

‘Yan wasan Mena ne suka haramtawa kasar Guinea shiga gasar a bana, a kwallayen da Mohammed Chikoto da Issoufou Garba suka zira a raga.

Sai dai duk da haka akwai babban kalubale a gaban Mena domin ‘yan wasan za su nemi fita kunya ne ba tare da magoya bayansu ba a birnin Port Elizabeth. Kamar yadda kocin Mena yace za su yi kokarin ba “Marada da kunya” duk da za su yi karon batta ne da wasu daga cikin manyan kasashe a Nahiyar Afrika. Yana me ba ‘yan wasan shi kwarin giwa su taka kwallo duk da sun san basu da magoya baya a filin wasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.