Isa ga babban shafi
FARANSA - nIJAR

Faransa ta fasa jibge dakarun da zata kwashe daga Mali a Nijar

Rundunar sojin Barkhane wadda Faransa ta kafa don yaki da ayyukan ta’addanci a yankin Sahel, ta ce babu batun kwashe sojojin kasar daga Mali zuwa Nijar kamar dai yadda aka yi hasashe bayan da Faransa ta ce za ta sauya wa dakarun matsuguni.

Sojojin Barkhane na Faransa da ke kawo karshen ziyarar aiki ta watanni hudu a yankin Gao da ke kasar Mali.
Sojojin Barkhane na Faransa da ke kawo karshen ziyarar aiki ta watanni hudu a yankin Gao da ke kasar Mali. © AP - Jerome Delay
Talla

Shugaban Rundunar ta Barkane Janar Laurent Michon ne ya sanar da wannan mataki a lokacin da yake zantawa da manema labarai a birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso, inda ya ce sam babu wannan zance na kwashe dakarun rundunar daga Mali zuwa Nijar.

Bayan shiga takun saka tsakaninsu da sojoji da ke kan karagar mulkin sojin kasar Mali, mahukuntan Faransa sun bayyana cewa za a janye dakarun daga Mali, tare da jibge su a wani wuri da ba a bayyana ba a lokacin.

To sai dai daga bisani mahukuntan kasar ta Faransa sun bayyana cewa sun cimma jituwa da takwarorinsu na jamhuriyar Nijar wadda ke cikin shiri domin karbar dakarun a kusa da kan iyakarta da Mali.

Shi dai janar Laurent Michon bai bayyana dalilan da suka sa mahukunta birnin Paris canza ra’ayi game da jibge wadannan sojoji da adadinsu ya zarta dubu 4 da 500 a Jamhuriyar Nijar ba, to sai dai y ace abu ne mai yiyuwa Faransa ta kara yawan dakarunta da ke cikin Nijar idan bukatar hakan ta taso a nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.