Isa ga babban shafi
Sahel-Faransa

Sojin Faransa sun hallaka dan ta'addan da ya kashe jami'an agaji a Nijar

Sojin Faransa da ke yaki da ta’addanci a yankin Sahel sun sanar da kisa wani gawurtaccen dan ta’adda da ke jagoranci kungiyar ISGS mai ikirarin jihadi a yammacin Afrika.

Dakarun Sojin Faransa da ke yaki da ta'addanci a yankin Sahel.
Dakarun Sojin Faransa da ke yaki da ta'addanci a yankin Sahel. defense.gouv.fr/operations
Talla

Dan ta’addan da aka bayyana sunansa da Soumana Bour ana cikin wadanda ake zargi da kisan jami’an agajin Faransa 6 a Jamhuriyyar Nijar cikin watan Agusta.

Majiyar tsaron Faransa ta ce dakarunta sun yi nasarar kisan Boura jagoran kungiyar ISGS ne a wani harin jirgi marar matuki lokacin da dan ta’addan ke tsaka da tafiya a kan babur mai kafa biyu.

Kungiyar IS dai ta dauki alhakin kisan jami’an agajin 6 wadanda faifan bidiyo ya nuno yadda aka yi musu yankan bayan da mayakan kungiyar suka kama su lokacin da su ke tsaka da ziyara a wani gandun daji a Nijar guda cikin kasashen yankin Sahel da ke fama da hare-haren ta’addanci.

Kakakin dakarun Faransa Kanal Pascal Ianni ya bayyana cewa sun gano Boura ne a cikin bidiyon kisan jami’an agajin na watan Agusta.

 A ranar 9 ga watan Agustan da ya gabata ne, ‘yan ta’addan suka yiwa jami’an agajin na Faransa 6 kisan gilla galibinsu ‘yan shekaru 26 zuwa 31 baya ga direbansu da kuma mai tsaron lafiyarsu lokacin da suke ziyara a gandun dajin Koure mai tazarar kilomita 60 daga Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.