Isa ga babban shafi

Harin ta'addanci ya kashe sojojin Nijar 7 a Diffa

Akalla sojojin Nijar 7 ne suka hallaka bayan da motarsu ta taka wata nakiya a yankin Diffa da ke kudu maso gabashin Jamhuriyar Nijar, inda kungiyoyi masu ikirarin jihadi ke addabar mutun yankin.

Wasu sojojin jamhuriyar Nijar da ke taimakawa Najeriya wajen yaki da kungiyar Boko Haram.
Wasu sojojin jamhuriyar Nijar da ke taimakawa Najeriya wajen yaki da kungiyar Boko Haram. AFP - PHILIPPE DESMAZES
Talla

Wata sanarwar soji da aka watsa a gidan rediyon kasar, tace fashewar ta auku ne da misalin karfe 12 na dare agogon GMT a kusa da wani sansanin soji da ke Chetimari Wangou mai tazarar kilomita 25 daga birnin Diffa.

Sanarwar ta ce, an kai sojoji biyu da suka zuwa wani asibiti dake Diffa domin kula da lafiyarsu.

Tafkin Chadi

Birnin Diffa na kusa da tafkin Chadi, wanda ya ratsa kan iyakokin Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi, inda tsagin mayakan Boko Haram wato ISWAP suka yi kaka gida.

Kasashe hudu da ke makwabtaka da tafkin sun kafa rundunar yaki da ta’addanci ta kasa da kasa a shekarar 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.