Isa ga babban shafi

Shirin ya duba yadda mata suka dukufa wajen neman aikin yi a Jamhuriyar Nijar

Shirin na yau ya tabo batun yadda mata ke fafutukar dogaro da kai, yayin da suke fama da rashin aikin yi a Jamhuriyar Nijar.

Mata da dama na bayar da gudun mowa ga rayuwar iyalansu ta fuskoki da dama.
Mata da dama na bayar da gudun mowa ga rayuwar iyalansu ta fuskoki da dama. REUTERS - Thierry Gouegnon
Talla

Wannan na zuwa ne yayin da alkaluman marasa aikin yi, musamman mata ke kara yawaita, daidai lokacin da ake ci gaba da samun rashin aikin yi a kasashe masu tasowa musamman na Afirka.

Masana tattalin arziki sun jima suna jan hankalin gwamnatoci game da muhimmancin samar da guraben ayyukan yi ga matasa, musamman mata, duba da cewa suna bayar da gagarumar gudun mowa ga cigaban rayuwar al'umma.

Latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin da Shamsiyya Haruna ta shirya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.