Isa ga babban shafi

Ana sa ran matasa suyi tasiri a zaben Najeriya

Al’ummar Najeriya musamman matasa na fatar ganin a wannan karo an zabo sabon shugaban da zai mayar da hankali wajen shawo kan matsalolin da suka addabi su musamman rashin ayyukan yi da rashin kula da makarantu yadda ya kamata da kuma kawo karshen yajin aikin malaman jama’o’i. 

Des responsables électoraux attendent de collecter du matériel électoral devant un poste de distribution à l'école primaire de Karewa à Yola, au Nigeria, le 25 février 2023.
Des responsables électoraux attendent de collecter du matériel électoral devant un poste de distribution à l'école primaire de Karewa à Yola, au Nigeria, le 25 février 2023. REUTERS - ESA ALEXANDER
Talla

A karon farko tun bayan kawo karshen mulkin soja a shekarar 1999, manyan ‘yan takara uku ne ke kalubalantar jam’iyya mai mulki wadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ke jagoranta a wannan zabe. 

Wani mazaunin birnin Lagos, Friday Ikwuako mai shekaru 55 da ke zabe a gundumar Ikoyi yace zaben zai banbanta a wannan karon, domin suna bukatar canji a gwamnati. 

An dai shirya bude rumfunan zabe da misalin karfe 8 na safiyar yau ne amma rahotanni daga sassa da dama sun ce an samu tsaiko wajen kai kayan aiki da kuma fara zaben, kamar yadda wakilanmu a Fatakwal da Maiduguri da Calabar da kuma Lagos suka shaida mana. 

Yayin da Buhari zai sauka daga mulki bayan wa’adi biyu a karagar mulki, ana saran dan takarar jam’iyyarsa Bola Tinubu  mai shekaru 70 kuma tsohon gwamnan Legas ya fafata da ‘dan takarar jam’iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, mai shekaru 76, wanda ke neman shugabanci a karo na shida tare da Peter Obi na jam’iyyar Labour da kuma Rabiu Musa Kwankwaso na Jam’iyyar NNPP. 

Karancin kudi da kuma karancin man fetur da ake fuskanta a makwannin da suka gabata kafin zaben ya kuma sa 'yan Najeriya da dama sun fusata a kasar da tuni ta fuskanci hauhawar farashin kayayyaki fiye da kashi 20 cikin dari. 

Najeriya ta kwashe shekaru tana fuskantar tashe-tashen hankula da rikicin kabilanci da addini, yayin da matsalar sayen kuri'u da fada tsakanin magoya bayan jam'iyyu ke barazana ga zaben shugaban kasar. 

Kusan sabbin masu kada kuri’a miliyan 10 ne suka yi rajista a wannan karo kuma yawancinsu matasa ne ‘yan kasa da shekara 34. 

Titunan Legas da sauran garuruwa sun kasance cikin kwanciyar hankali yayin da aka hana zirga-zirga domin ganin an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali. 

Haka kuma 'yan kasar za su kada kuri’unsu na ‘yan majalisun dokokin Najeriya guda biyu, wato majalisar wakilai da ta dattawa.  

A Fatakwal, kusan mazabu guda 6 ne suka kasance ba tare da an fara zaben ba lokacin da wakilinmu Michael Kuduson ya ziyarci wuraren. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.