Isa ga babban shafi

Najeriya na iya fuskantar zaben shugaban kasa zagaye na biyu

An gudanar da zaben shugaban kasa a Najeriya,kasa da ta fi kowacce yawan jama’a a nahiyar Afirka, kasar tsawon shekaru ta yi fama da matsalolin da dama,yayinda zaben na yau ya fuskanci jinkiri da dama da ke iya haifar da fushi a tsakanin wasu masu kada kuri’a.

Yadda wasu masu kada kuri'a ke neman sunayensu gabanin kadda kuri'a a Lagos (2023/02/25)
Yadda wasu masu kada kuri'a ke neman sunayensu gabanin kadda kuri'a a Lagos (2023/02/25) AP - Mosa'ab Elshamy
Talla

Najeriya  ta yi fama da matsalar rashin tsaro da fatara a yan shekaru  nan da kashi 60% na al’ummar kasar ‘yan kasa da shekara 25, shugaban kasa Muhammadu Buhari mai shekaru 80 zai sauka daga mulki kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

Kuma a karon farko tun bayan komawar mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999, farin jinin wani daga waje yana girgiza rinjayen manyan jam'iyyu biyu kuma Najeriya na iya fuskantar zaben shugaban kasa zagaye na biyu.

Osaki Briggs, wani mai daukar hoto mai shekaru 25 da ya zo zabe a Fatakwal (kudu maso gabas) tare da matarsa, ya shaida wa AFP cewa, "Akwai matsin lamba sosai a wannan shekara dangane da batun zabe."

“A wannan karon an yi mana alkawarin cewa za a gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci, don haka fatanmu ya kasance haka.

Sama da masu kada kuri’a miliyan 87 ne za su kasance a rumfunan zabe 176,000 domin zabar shugaban kasa daga cikin ‘yan takara 18, da kuma mataimaka da ‘yan majalisar dattawa. 

An dai ci gaba da kada kuri’a cikin lumana gaba daya, amma a wurare da dama, kamar Legas (kudu maso yamma) ko kuma Kano (arewa), an dauki lokaci mai tsawo saboda kayan aiki ba su iso ba ko kuma ba sa aiki, in ji ‘yan jaridar AFP.

Wannan shi ne karo na farko da aka yi amfani da sabbin fasahohi a ma'aunin kasa. Gano masu jefa ƙuri'a ta fuskar fuska da na dijital ya kamata ya iyakance zamba da ya lalata zaben da ya gabata.

"Ba wanda ya damu da mu! Na isa karfe 8 na safe kuma yanzu karfe 12 na rana kuma na'urar ba ta aiki," in ji Jennifer Dike, ma'aikaciyar gwamnati mai shekaru 28 a wani rumbun zabe a Fatakwal, a cikin wani yanayi mai zafi. "Ya kamata su bar mu mu kada kuri'a da hannu, muna da PVCs (katin zabe).. Amma babu wanda ya yi wani abu!".

A wani taron manema labarai, Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (Inec) Farfesa Mahmood Yakubu, ya amince da "matsalolin", yayin da ya tabbatar da cewa "duk dan Najeriya da ke kan layi zai samu damar kada kuri'a komai tsawon lokaci," duk da jadawalin da aka tsara,za a kuma rufe ruhunan zabe da misamin karfe 2:30 na rana.

Tafiyar Bola Ahmed Tinubu

Dan takarar jam’iyyar APC mai mulki, Bola Tinubu, mai shekaru 70, sanye da rigar  shudi, ya kada kuri’a a safiyar asabar a mazabar sa da ke Legas inda ya samu tarbar jama’a da rakiyar jami’an tsaro.

Ana yi wa Bola Tinubu tsohon Gwamna (1999-2007) lakabi da “Ubangiji” saboda tasirin siyasarsa.

Yarbawa mabiya addinin musulunci, sun yi ikirarin cewa shi kadai ne zai iya gyara Najeriya kuma ya riga ya yi gargadin cewa: “Lokaci na ne” in yi mulki.

Atiku,sabuwar tafiya

A bangaren  abokan hamayyarsa guda biyu,dan shekaru 76, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, na jam'iyyar adawa (PDP, mai mulki daga 1999 zuwa 2015), zai sake tsayawa takarar shugaban kasa a karo na shida,sai tsohon gwamnan Anambra (kudu-maso-gabas) Peter Obi, mai shekaru 61 kirista, wanda karamar jam’iyyar Labour (LP) ke marawa baya, kuma ya shahara a wajen matasa.

Najeriya za ta  zama kasa ta uku mafi yawan al'umma a duniya nan da shekarar 2050, yayin da yammacin Afirka ke fuskantar barazanar koma bayan dimokuradiyya da kuma yaduwar tashin hankalin daga kungiyoyi masu ikirarin jihadi.

Kasar da ta fi karfin tattalin arzikin nahiyar ta zama wata kasa mai karfin al'adu ta duniya, musamman bangaren waka na Afrobeats, wani nau'in kade-kade da ke tashe a duniya da irin taurari irinsu Burna Boy da Wizkid.

Amma shugaban kasa na gaba zai gaji dimbin matsaloli: tashin hankalin masu laifi da na jihadi a arewa da tsakiya, tashin hankalin ‘yan aware a kudu maso gabas, hauhawar farashin kayayyaki, talauci mai yaduwa.

Babban abin da ya fi muni shi ne, karancin man fetur da takardun kudi na baya-bayan nan ya haifar da tarzoma.

"Najeriya babbar matsala ce, muna bukatar shugabannin da suka cancanta a wannan yanayin," in ji Fasto John Fashugba, mai shekaru 76, wanda ya dauki zaben a matsayin "mafi mahimmanci" da ya sani.

A duk fadin kasar, an kuma sha fama da hare-haren da ake kai wa 'yan takara na cikin gida, da masu fafutuka, da ofisoshin 'yan sanda da kuma ofisoshin hukumar zabe.

"Hadarin tashin hankali abin damuwa ne," in ji Sa'eed Husaini na Cibiyar Dimokuradiyya da Ci Gaba (CDD).

Shiga, ƙananan a zabukan da suka gabata (33% a 2019) wani abu ne da ba a sani ba.

Za  fitar da sakamakon zaben a hukumance a cikin kwanaki 14 bayan wannan zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.