Isa ga babban shafi
FARANSA

‘Yan majalisun Romania sun soki Gwamnatin Faransa

‘Yan majalisun kasar Romaniya sun yi kakkausar suka ga gwamnatin kasar Faransa na keta hakkin ‘yan kasar Romaniya na zama ‘yan kasa.‘Yan Majalisar Wakilai da Majalisar dattijan kasar sun bayyana bakin cikinsu ga hukuncin da gwamnatin kasar Faransa ta dauka kan ‘yan kasar  dake zaune a cikin kasar Faransa wadanda kuma ke da hakkin zama ‘yan kasar.''Yan majalisun sun Umurci Shugaban kasar Romaniya Traian Basescu da ya dauki matakai na kare hakkin ‘Yan kasar a ko ina na fadin duniya. An dai bayyana cewa Al’ummar Romaniya sune mafiya yawa a nahiyar Turai inda kididdigar da aka gudanar ya nuna cewa al’ummar Romaniya sun tasan ma mutane sama 530,000.A 29 ga watan satumba ne ake saran kungiyar Tarayyar turai ta yanke hukunci kan kasar Faransa na Bijerewa Umurnin kungiyar. 

'Yan kasar Romaniya
'Yan kasar Romaniya Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.