Isa ga babban shafi
Birtaniya

Blair ya amince kan bada goyon bayan yakin Iraqi

Yayin da ya gurfana gaban kwamitin binciken Birtaniya a yau juma’a, Tsohon Fira Minstan kasar Tony Blair ya amsa cewa ya dauki alkawali don taimakon shugaban kasar Amurka George Bush kan karya Saddam Hussain duk da adawa da bangaren sha’riar kasar ya nuna da matakin nasa.Daga cikin bayanan da tsohon Fira minitan ya gabatarwa kwamitin binciken, Blair yace ya goyi bayan shugaban Amurka George Bush tare da bashi kwarin gwiwar cewa Birtaniya zata yi duk abinda ya dace wajen ganin karya Saddam Hussain.A bayanin nasa tsohon shugaban yace ya nemi shawarar tsohon babban mai shari’a a kasar Peter Goldsmith a 14 ga watan Janairun shekarar 2003 wanda ya ba shi shawarin cewa yana da kyau ya jira matakin da majalisar Dunkin Duniya ta dauka kafin yanke wannan hukuncin.Sai dai kuma tsohon Fira ministan yace daga baya ne Goldsmith ya canza shawara daga matakinsa na farko. Inda Blair yace da ace Peter Goldsmith bai canza shawarsa ba da Birtaniya bata saka hannu ga matakin karya Saddam Hussain ba.Yayin  gurfanar da shugaban a bara, Mista Blair yace sam baya da wata fargaba ga hukuncin da aka yankewa tsohon shugaban Iraki Saddam Hussain tare da bayyana cewa kawar da Saddam shi zai kara kawo zaman lafiya a duniya.Kwararan matsakan tsaro ne dai aka dauka Yayin zaman binciken tsohon shugaban, kodayake gungun masu zanga zanga ne suka yi gangami rike da takardu masu dauke da bayanin sunan ‘Bliar’.  

Tsohon Fira Ministan Birtaniya Tony Blair
Tsohon Fira Ministan Birtaniya Tony Blair REUTERS/UKBP
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.