Isa ga babban shafi
EU-Birtaniya

Birtaniya ta yi barazanar fatali da sabuwar yarjejeniyar Turai

Fira Ministan Birtaniya, David Cameron, ya yi barazanar fatali da sabbbin kudirorin kungiyar kasashen Turai, da aka shirya don ceto kudin Euro, idan aka ki amincewa da bukatun kasar na farfado da kasuwar hannayen jarin Turai.

Amintaka ta yi kamari tsakanin Fira Ministan Birtaniya tsakanin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel
Amintaka ta yi kamari tsakanin Fira Ministan Birtaniya tsakanin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel Reuters/Tobias Schwarz
Talla

Cameron yace ya zama dole dokar ta kare hukumomin kudin kasar da kuma kasuwanninta, kafin ya sanya hannu akan yarjejeniyar ceto Euro, kudin da Birtaniya bata amfani da shi.

Wannan barazanar ta Birtaniya na nuna cewa, a karshe kasashen Faransa da Jamus na iya mayar da yarjejeniyar ta koma ta kasashe 17 da ke amfani da kudin Euro maimakon daukacin kasashe 27 na Turai.

Tun da farko dai kasashen Faransa da Jamus sun bukaci kafa wata sabuwar yarjejeniya a watan Mayu ta zata tsaurara matakan tsuke bakin aljihun gwamnati tare da katse kasafin kudaden kasashen Turai.

Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy yace sabuwar yarjejeniyar zata iya shafar kasashen kungiyar Tarayyar Turai 27 ko kasashe 17 mambobin kungiyar masu amfani da kudin euro.

Sai dai Cameron yace idan har kasashen suka amince da kafa sabuwar yarjejeniyar mataki ne da Birtaniya zata kauracewa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.