Isa ga babban shafi
Faransa

Sarkozy ya yi alkawalin ci gaba da aiwatar da sauye-sauye

Kwanaki Biyu bayan rage darajar basukan kasar Faransa, shugaba Nicolas Sarkozy, ya yi alkawarin ci gaba da aiwatar da sauye sauyen tattalin arziki, don mayar da darajar kasar da kokarin fitar da ita daga cikin rikici.Shugaba Sarkozy ya yi alkawarin yin jawabi ga ‘Yan kasar a karshen watan Janairu, inda zai bayyana matakan da zai dauka, don magance matsalar.

Nicolas Sarkozy Shugaban kasar Faransa
Nicolas Sarkozy Shugaban kasar Faransa Reuters/Charles Platiau
Talla

Watanni uku ne dai ya rage a gudanar da zaben shugaban kasa a Faransa, amma Sarkozy yace dole ne gwamnatinsa ta fito da karfinta domin warware rikicin tattalin arziki.

A ranar Laraba ne ake sa ran shugaban zai tattauna da kungiyoyin kwadago da fararen hula domin tattauna samar da aiki yi a cikin kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.