Sarkozy ya kwarmata kudirin yin tazarce a Faransa
Shugaban Kasar Faransa, Nicolas Sarkozy, ya kwarmata shirin yin tazarce a zaben shugaban kasa da za’a yi a watan Afrilu, bayan an dade ana rade radin tsayawar shugaban takara. Sai dai shugaban bai fito fili ya bayyana kudirin yin takarar ba.
Wallafawa ranar:
A wata hira da ya yi da manema labarai, shugaba Sarkozy yace, akwai alkawari tsakanin shi da Faransawa, saboda haka babu yadda zai gudu ba tare da cika alkawalin ba, wajen kokarin magance matsalolin da ke addabar kasar da suka hada da tattalin arziki
Shugaban ya bayyana Karin kudin haraji daga sama da kashi daya da rabi, zuwa sama da kashi 21, wanda ake saran zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Octoba mai zuwa.
Shugaba Sarkozy wanda ya kudurta farfado da darajar tattalin arzikin Faransa, yanzu haka akwai kalubalen magance matsalar rashin aikin yi a kasar da dimbim basukan da ake bin Faransa.
Wannan fitowar ta Sarkozy na zuwa ne mako guda bayan abokin hamayyarsa Hollande ya kaddamar da yakin neman zabensa inda ya yi kakkausar suka ga matakan da shugaban ya dauka wajen warware matsalar tattalin arziki.
Wani zaben jin ra’ayin Jama’a da aka gudanar ya nuna Hollande ne zai lashe zaben shugaban kasa da rinjayen kuri’u kashi 56 cikin 100 inda kuma Sarkozy ya samu kuri’u kashi 44.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu