Isa ga babban shafi
Norway

Mutumin da ya hallaka mutane 77 a Norway ya nemi lambar yabo

Anders Behring Breivick, mutumin da ya hallaka mutane 77 a kasar Norway, ya bukaci kotu ta bashi lambar girma, tare da sakin shi don ya kama gaban shi bayan zaman kotu a jiya Litinin.

Anders Behring Breivik,Mutumin da ya kashe mutane 77 a birnin 'Oslo.
Anders Behring Breivik,Mutumin da ya kashe mutane 77 a birnin 'Oslo. Reuters / Lise Aserud
Talla

Mista Breivik, yace harin da ya kai ranar 22 ga watan Yuli, hari ne kan maciya amana, wadanda ke karbar baki, don yada addinin Islama a kasar Norway.

Ya kuma amsa sanya bom da bude wuta ga matasa, amma yace wannan ba laifi ba ne inda kalaman nasa suka haifar da sowa a zaman kotun.

Behring Breivik wanda ke ikirarin kaddamar da yaki akan musulmi, a ranar 22 ga watan Juni ne ya dala bom a wata mota wanda ya yi sanidyar mutuwar mutane 8 nan take a birnin Oslo.

Daga bisani ne ya tsere zuwa tsibirin Uteoya da ke arewa maso yammacin birnin Oslo inda ya yi shigar ‘yan sanda tare da bude wauta ga wasu mutane 69 yawancinsu matasa.

An dangata wannan al’amari a matsayin mafi muni a kasar Norway tun bayan yakin Duniya na biyu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.