Isa ga babban shafi
Faransa-Masar

Sarkozy ya haramta wa Qaradawi Ziyara a Faransa

Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy yace kasar Faransa ba zata karbi bakuncin Malamin Sunni Yusuf al- Qaradawi bayan kungiyar ‘Yan uwa musulmin Faransa sun aika masa da sakon gayyata.

Sheikh Yusuf al-Qaradawi lokacin da yake ziyara a Taron kasashen Duniya game da birnin Kudus a Doha
Sheikh Yusuf al-Qaradawi lokacin da yake ziyara a Taron kasashen Duniya game da birnin Kudus a Doha Reuters/Mohammed Dabbous
Talla

Shugaba Sarkozy yace ya aikawa Sarkin Qatar sakon rashin amincewa da ziyarar Qaradawi.

Malam Qaradawi dan asalin kasar Masar ne mai gabatar da shiri a kafar Telebijin ta AlJazeera da ke goyon bayan juyin juya halin kasashen larabawa a kasashen Tunisia da Masar da Libya tare da bayar da Tallafi ga ‘Yan adawar kasar Syria.

A ranar shida ga watan Afrilu ne Qaradawi zai kai ziyara wani taron musulunci a Faransa tare da malamin kasar Masar Mahmoud al Masri.

Sarkozy yace akidar Qaradawi ta sabawa Jamhuriyyar Faransa don haka ba zasu amince da ziyarar Malamin ba.

Qaradawi dai ya dade yana fuskantar kalubale daga kasashen Yammaci, domin a shekarar 2008 Birtaniya ta haramta masa shiga kasar bayan Amurka ta haramta masa kai ziyara a shekarar 1999.

Sai dai Kungiyar Musulmi ta duniya karkashin Jagorancin Sheikh Yusuf al-Qaradawi sun yi Allah waddai da matakin haramtawa Shaihin Malamin kai ziyara kasar Faransa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.