Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta kori wasu malaman Musulunci 5 daga cikin kasar

Gwamnatin Kasar Faransa ta koro wasu ‘yan kasashen waje biyar da ake zargin masu tsatstsaurar ra’ayin addinin musulunci ne, a wani ynkuri da kasar ke yi na share ta’adanci bayan bulluwar dan bindigar da ya kashe mutane bakwai a Toulouse.

Nicolas Sarkozy Shugaban kasar Faransa
Nicolas Sarkozy Shugaban kasar Faransa
Talla

Ma’aikatar Harkokin cikin gidan Faransa tace akwai mutane biyu masu tsatstsauran ra’ayin addini Islama, da suka hada da wani limami dan kasar Mali da wani dan kasar Algeria, wadanda aka fitar dasu daga Faransa zuwa kasashensu.

Ma’aikatar tace akwai kuma wasu mutane uku, da suka hada da wani Malamin kasar Saudiyya, da dan kasar Turkiyya, da wani dan kasar Tunisia da za’a sake kora daga Faransa.

Laifin mutanen, inji sanarwan shi ne gudanar da wa’azin da ke kyamatar dabi’un kasashen Turai, tare da kira ga mata wajen suturta jikinsu da nikab da aka haramta a fadin kasar Faransa.

A ranar Juma’ar makon jiya ‘Yan sandan Faransa sun kama mutane akalla 19, a wani samame da suka kai domin farautar wadanda ake ganin suna iya kitsa ayyukan ta’addanci, a kokarin da Shugaba Nicolas Sarkozy yace yana daga cikin abubuwan da zai bada karfi a wa’adin mulkinsa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.