Idan Moody ya rage darajar Faransa laifin Sarkozy ne, inji Hollande
Dan Takarar shugabancin kasar Faransa, Francois Hollande, ya shaidawa Rediyo Faransa cewa idan kamfanin da ke rage darajar cin bashi na Moody ya rage darajar kasar Faransa bayan zaben watan Mayu, zai kasance laifin shugaba Nicolas Sarkozy idan har ya gaji gwamnatinsa.
Wallafawa ranar:
Hollande wanda shi ne babban mai hamayya da Sarkozy a zaben shugaban kasa yace kamfanin Moody yana amfani ne da bayanan da ya tattara, kuma Kamfanin ya yi gargadin zai rage darajar biyan bashin kasar Faransa.
A cewar Hollande, duk wani mataki da zai fito bayan zaben shugaban kasa, zai zama abinda gwamnati mai barin gado ne ta yi.
Mako daya ne ya rage a jefa kuri’ar zaben shugaban kasa zagaye na farko a Faransa kuma Hollande yace zai inganta tattalin arzikin kasar idan ya lashe zabe.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu